2 Tarihi 25:17-24
17
Bayan Amaziya sarkin Yahuda ya nemi shawara mashawartansa, sai ya kalubalanci Yowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, “Zo mu gamu fuska da fuska.”
18
Amma Yowash sarkin Isra’ila ya amsa wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika da saƙo wa itacen al’ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Sai wani naman jeji na Lebanon ya zo ya tattake ƙayar.
19
Ka ce wa kanka cewa ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana fariya da ɗaga kai. Amma tsaya dai a gida! Me ya sa kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da ta Yahuda?”
20
Amma Amaziya bai saurara ba gama Allah ya yi haka domin yă miƙa su ga Yehowash, domin sun nemi shawarar allolin Edom.
21
Saboda haka Yowash sarkin Isra’ila ya kai yaƙi. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh a Yahuda.
22
Isra’ila ta fatattaki Yahuda, sai kowane mutum ya gudu zuwa gidansa.
23
Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya kawo shi Urushalima ya farfasa katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, wani sashe mai tsawon ƙafa ɗari shida.
24
Ya kwashe dukan zinariya da azurfa da dukan kayayyakin da aka samu a haikalin Allah waɗanda suke a ƙarƙashin kulawar Obed-Edom, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.
Settings