2 Tarihi 2:11
Ana nuna aya 11 tare da mahallin da ke kewaye.
8
“Ka kuma aika mini al’ul, fir da gumaguman algum daga Lebanon, gama na san cewa mutanenka sun gwanince a yakan katakai a can. Mutanena kuwa za su yi aiki tare da naka
9
don su tanada mini katakai da yawa, domin haikalin da zan gina dole yă zama mai girma da kuma ƙasaitacce.
10
Zan ba wa bayinka masu yankan katakai waɗanda suka yanka katako, garwa niƙaƙƙen alkama dubu ashirin, garwan sha’ir dubu ashirin da randunan ruwan inabi dubu ashirin da kuma randunan man zaitun dubu ashirin.”
11
Hiram sarkin Taya ya amsa ta wurin rubuta wasiƙa zuwa ga Solomon. “Domin Ubangiji yana ƙaunar mutanensa, ya naɗa ka sarkinsu.”
12
Hiram ya ƙara da cewa, “Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa! Ya ba Sarki Dawuda ɗa mai hikima, cike da wayo da kuma sani, wanda zai gina haikali domin Ubangiji da kuma fada wa kansa.
13
“Zan aika maka Huram-Abi, wani gwani wanda ya iya aiki, kuma mai hikima,
14
wanda mahaifiyarsa ta fito daga Dan, mahaifinsa kuma daga Taya. An horar da shi a aikin zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, dutse, itace, da kuma shuɗi, shunayya, garura, da lilin mai kyau. Ya gogu a kowane irin zāne-zāne, zai kuma iya yin kowane zānen da aka ba shi. Zai yi aiki tare da masu sana’arka, da kuma tare da waɗanda ranka yă daɗe, Dawuda mahaifinka ya tanada.
Settings