Skip to content
2 Tarihi 2:11-16

2 Tarihi 2:11-16

11
Hiram sarkin Taya ya amsa ta wurin rubuta wasiƙa zuwa ga Solomon. “Domin Ubangiji yana ƙaunar mutanensa, ya naɗa ka sarkinsu.”
12
Hiram ya ƙara da cewa, “Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa! Ya ba Sarki Dawuda ɗa mai hikima, cike da wayo da kuma sani, wanda zai gina haikali domin Ubangiji da kuma fada wa kansa.
13
“Zan aika maka Huram-Abi, wani gwani wanda ya iya aiki, kuma mai hikima,
14
wanda mahaifiyarsa ta fito daga Dan, mahaifinsa kuma daga Taya. An horar da shi a aikin zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, dutse, itace, da kuma shuɗi, shunayya, garura, da lilin mai kyau. Ya gogu a kowane irin zāne-zāne, zai kuma iya yin kowane zānen da aka ba shi. Zai yi aiki tare da masu sana’arka, da kuma tare da waɗanda ranka yă daɗe, Dawuda mahaifinka ya tanada.
15
“Yanzu fa, bari ranka yă daɗe, yă aiko wa bayinsa alkama da sha’ir da kuma man zaitun da ruwan inabin da ka alkawarta,
16
za mu kuwa yanka dukan gumagumai daga Lebanon da kake bukata za mu kuwa yi fitonsu ta teku, su gangara zuwa Yaffa. Za ka iya kwashe su daga can ka haura zuwa Urushalima.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options