Skip to content
1 Tessalonikawa 1:6-10

1 Tessalonikawa 1:6-10

6
Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar.
7
Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya.
8
Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne ko’ina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai,
9
gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya,
10
ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options