1 Tessalonikawa 1:2-5
2
Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu.
3
Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.
4
Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku,
5
domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku.
Settings