Skip to content
1 Sama’ila 7:9-14

1 Sama’ila 7:9-14

9
Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.
10
Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa.
11
Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar.
12
Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.”
13
Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila.
14
Filistiyawa suka mayar wa Isra’ila da garuruwan da suka ƙwato, wato, daga Ekron zuwa Gat, dukan yankin ƙasarsu da yake ƙarƙashin ikon Filistiyawa. Aka kuma sami zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Amoriyawa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options