1 Sama’ila 7:5-12
5
Sama’ila ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ila a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.”
6
Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.
7
Da Filistiyawa suka ji cewa Isra’ila sun taru a Mizfa, sai shugabanninsu suka zo don su yaƙe Isra’ila. Da Isra’ilawa suka ji labarin, sai suka tsorata saboda Filistiyawa.
8
Suka ce wa Sama’ila, “Kada ka fasa kai kukanmu ga Ubangiji Allahnmu saboda mu, don yă cece mu daga hannun Filistiyawa.”
9
Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.
10
Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa.
11
Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar.
12
Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.”
Settings