Skip to content
1 Sama’ila 23:23-29

1 Sama’ila 23:23-29

23
Ku binciko duk wuraren da yakan ɓuya, sai ku dawo ku gaya mini tabbataccen labari. Sa’an nan zan tafi tare da ku in yana can. Zan nemi shi ko’ina cikin dukan kabilar Yahuda.”
24
Sai suka tashi suka koma Zif, suka sha gaban Shawulu. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon cikin Araba, kudu da Yeshimon.
25
Shawulu da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya gangara cikin duwatsu ya zauna a cikin jejin Mawon. Sa’ad da Shawulu ya ji haka, sai ya tafi jejin Mawon yana fafaran Dawuda.
26
Shawulu yana tafiya a gefe ɗaya na dutsen, Dawuda da mutanensa kuma suna a wancan gefe, suna hanzari su ɓace wa Shawulu. Sa’ad da Shawulu da sojojinsa suka kusa cimma Dawuda da mutanensa don su kama su,
27
sai wani manzo ya zo wurin Shawulu yana cewa, “Ka koma da sauri, Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”
28
Shawulu kuwa ya janye daga fafaran Dawuda, ya tafi yă ƙara da Filistiyawa. Dalilin ke nan da ake kiran wannan wuri Sela Hammalekot, wato, dutsen tserewa.
29
Dawuda kuwa ya haura daga can ya zauna a kogwannin duwatsun En Gedi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options