Skip to content
1 Sama’ila 16:14-23

1 Sama’ila 16:14-23

14
To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala.
15
Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala.
16
Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.”
17
Saboda haka Shawulu ya ce wa ma’aikatansa, “Ku nemo wanda ya iya kiɗan molo sosai ku kawo mini.”
18
Ɗaya daga cikin bayin ya ce, “Na san wani yaro, ɗan Yesse na Betlehem, ya iya kiɗan molo, yana da hikima, shi kuma ya iya yaƙi. Ya iya magana, ga shi kuma kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”
19
Sai Shawulu ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka Dawuda wanda yake kiwon tumaki.”
20
Saboda haka Yesse ya ɗauki jaki tare da burodi da ruwan inabi da ɗan ƙarami bunsuru ya ba wa ɗansa Dawuda yă kai wa Shawulu.
21
Dawuda ya isa wurin Shawulu ya shiga hidimarsa. Shawulu kuwa ya so shi ƙwarai da gaske. Dawuda ya zama ɗaya daga cikin masu sanya sulke.
22
Sa’an nan Shawulu ya aika saƙo wurin Yesse cewa, “Ka bar Dawuda yă yi mini hidima domin ina jin daɗinsa ƙwarai.”
23
Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options