1 Sarakuna 4:22-28
22
Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci,
23
shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
24
Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe.
25
A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa.
26
Solomon yana da rumfunan dawakai masu jan kekunan yaƙi, dubu huɗu, da kuma dawakai dubu goma sha biyu
27
Shugabannin yankuna, kowanne a watansa yakan yi tanajin abinci domin Sarki Solomon da kuma duk wanda ya zo teburin sarki. Sun tabbatar ba a rasa kome ba.
28
Kowa a cikinsu, bisa ga lokacin da aka ba shi, yakan kai hatsin sha’ir da ciyawa domin dawakan-kekunan yaƙi, da sauran dawakai a inda aka ajiye su.
Settings