1 Sarakuna 11:1-13
1
Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa.
2
Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu.
3
Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi.
4
Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba.
5
Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.
6
Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba.
7
A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.
8
Ya yi haka domin dukan baƙin matansa, waɗanda suka ƙone turare suka kuma miƙa hadayu ga allolinsu.
9
Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu.
10
Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba.
11
Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka.
12
Amma saboda Dawuda mahaifinka, ba zan yi haka a zamaninka ba. Zan yage ta daga hannun ɗanka.
13
Amma ba zan yage dukan masarautar daga gare shi ba, zan ba shi kabila ɗaya saboda Dawuda bawana, da kuma saboda Urushalima, wadda na zaɓa.”
Settings