- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Fasikancin jima'i yana ƙazantar da jiki
1 Korintiyawa 6:12-20
12
“Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni.
13
“An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.
14
Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma.
15
Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam!
16
Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.”
17
Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.
18
Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.
19
Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;
20
saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
Settings