- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
1 Korintiyawa 15:12-34
12
Amma in ana wa’azi cewa Kiristi ya tashi daga matattu, yaya waɗansu a cikinku suke cewa babu tashin matattu?
13
In babu tashin matattu, to, ba a tā da Kiristi ma ba ke nan.
14
In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, wa’azinmu, da bangaskiyarku banza ne.
15
Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a tā da matattu.
16
Gama in ba a tā da matattu ba, to, Kiristi ma ba a tashe shi ba ke nan.
17
In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan.
18
Ashe, waɗanda suka yi barci a cikin Kiristi ma sun hallaka ke nan.
19
In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane.
20
Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci.
21
Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum.
22
Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi.
23
Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa.
24
Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko.
25
Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.
26
Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.
27
Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi.
28
Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome.
29
To, in babu tashin matattu, mene ne waɗanda ake musu baftisma saboda matattu za su yi? In ba a tā da matattu sam, me ya sa ake yin wa mutane baftisma saboda su?
30
Mu ma don me muke sa kanmu cikin hatsari a kowace sa’a?
31
Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
32
In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga ra’ayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a tā da matattu? Ai, “Sai mu ci mu sha, da yake gobe za mu mutu.”
33
Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”
34
Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba, na faɗi wannan ne don ku kunyata.
Settings