1 Korintiyawa 11:18-34
18
Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.
19
Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.
20
Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba,
21
gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu.
22
Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!
23
Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi,
24
bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.”
25
Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.”
26
Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo.
27
Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan.
28
Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin.
29
Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne.
30
Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci.
31
Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba.
32
Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.
33
Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna.
34
In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci. Sa’ad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai.
Settings