Skip to content
1 Korintiyawa 10:1-13

1 Korintiyawa 10:1-13

1
Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku.
2
An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku.
3
Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda
4
suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne.
5
Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada.
6
To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.
7
Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”
8
Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu.
9
Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su.
10
Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su.
11
Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.
12
Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!
13
Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options