Skip to content
1 Tarihi 9:1-22

1 Tarihi 9:1-22

1
Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila. Aka kwasa mutanen Yahuda zuwa zaman bauta a Babilon domin rashin aminci.
2
To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali.
3
Waɗanda suke daga Yahuda, daga Benyamin, da kuma daga Efraim da Manasse waɗanda suka zauna a Urushalima su ne,
4
Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda.
5
Na mutanen Shilo kuwa su ne, Asahiya ɗan fari da ’ya’yansa maza.
6
Na mutanen Zera su ne, Yewuyel. Mutane daga Yahuda sun kai 690.
7
Na Benyamin su ne, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Hodawiya, ɗan Hassenuwa;
8
Ibnehiya ɗan Yeroham; Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya.
9
Mutane daga Benyamin, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, sun kai 956. Dukan waɗannan mutane kawunan iyalansu ne.
10
Na firistoci su ne, Yedahiya; Yehoyarib; Yakin;
11
Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah;
12
Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya; da Ma’asai ɗan Adiyel, ɗan Yazera, ɗan Meshullam, ɗan Meshillemit, ɗan Immer.
13
Firistocin da suke kawunan iyalai, sun kai 1,760. Dukansu ƙwararru ne, masu hakkin hidima a cikin gidan Allah.
14
Na Lawiyawa su ne, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, mutumin Merari;
15
Bakbakkar, Heresh, Galal da Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zikri, ɗan Asaf;
16
Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun; da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa.
17
Matsaran ƙofofi su ne, Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da ’yan’uwansu. Shallum ne babbansu
18
da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa.
19
Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da ’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji.
20
A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi.
21
Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.
22
Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options