1 Tarihi 8:29-38
29
Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Sunan matarsa Ma’aka,
30
ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,
31
Gedor, Ahiyo, Zeker
32
da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
33
Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
34
Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda ya zama mahaifin Mika.
35
’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tereya da Ahaz.
36
Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
37
Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel.
38
Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan ’ya’yan Azel maza ne.
Settings