1 Tarihi 7:20-29
20
Zuriyar Efraim su ne, Shutela, Bered, Tahat, Eleyada, Tahat
21
Zabad da Shutela. Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu.
22
Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.
23
Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.
24
’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce,
25
Refa, Reshef, Tela, Tahan,
26
Ladan, Ammihud, Elishama,
27
Nun da kuma Yoshuwa.
28
Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta.
29
A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.
Settings