Skip to content
1 Tarihi 7:14-19

1 Tarihi 7:14-19

14
Zuriyar Manasse su ne, Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad.
15
Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa. ’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da ’ya’yan mata ne kawai.
16
Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh, ’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem.
17
Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse.
18
’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala.
19
’Ya’yan Shemida maza su ne, Ahiyan, Shekem, Liki da Aniyam.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options