1 Tarihi 21:1-8
1
Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila.
2
Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.”
3
Amma Yowab ya amsa ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya mayaƙansa fiye da sau ɗari. Ranka yă daɗe sarki, dukansu ba bayin shugabana ba ne? Me ya sa ranka yă daɗe yake so yă yi haka? Me zai sa ka kawo laifi a kan Isra’ila?”
4
Amma sarki ya nace a kan maganar da ya yi wa Yowab. Sai Yowab ya tashi ya tafi cikin dukan Isra’ila, ya kewaye sa’an nan ya dawo Urushalima.
5
Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.
6
Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.
7
Wannan umarnin mugu ne a gaban Allah; saboda haka ya hukunta Isra’ila.
8
Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai ta wurin yin wannan. Yanzu, na roƙe ka, ka ɗauke laifin bawanka. Na yi wauta sosai.”
Settings