Skip to content
1 Tarihi 16:8-22

1 Tarihi 16:8-22

8
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
9
Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
10
Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
11
Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.
12
Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,
13
Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.
14
Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya.
15
Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
16
alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.
17
Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.
18
“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.”
19
Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
20
suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan.
21
Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna.
22
“Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options