1 Tarihi 16:37-43
37
Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.
38
Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.
39
Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon
40
don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.
41
Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
42
Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.
43
Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.
Settings