1 Tarihi 16:23-33
23
Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.
24
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.
25
Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
26
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai.
27
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.
28
Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,
29
ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.
30
Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.
31
Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”
32
Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!
33
Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya.
Settings