1 Tarihi 12:1-16
1
Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi;
2
suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su ’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin):
3
Ahiyezer babbansu da Yowash ’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya; Yeziyel da Felet ’ya’yan Azmawet; Beraka, Yehu daga Anatot,
4
da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin; Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera,
5
Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf;
6
Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora;
7
da Yoyela da Zebadiya ’ya’yan Yeroham maza daga Gedor.
8
Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.
9
Ezer shi ne babba, Obadiya shi ne mai binsa a shugabanci, Eliyab na uku,
10
Mismanna na huɗu, Irmiya na biyar,
11
Attai na shida, Eliyel na bakwai,
12
Yohanan na takwas, Elzabad na tara,
13
Irmiya na goma da kuma Makbannai na goma sha ɗaya.
14
Waɗannan mutanen Gad shugabannin mayaƙa ne; ƙarami a cikinsu zai iya ƙara da mutum ɗari, kuma babba a cikin zai iya ƙara da dubu.
15
Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma.
16
Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa.
Settings