Skip to content
1 Tarihi 11:1-9

1 Tarihi 11:1-9

1
Dukan Isra’ila fa suka taru wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu jiki da jininka ne.
2
A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’ ”
3
Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila.
4
Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin
5
suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda.
6
Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba.
7
Dawuda zauna a kagarar, ta haka aka kira ta Birnin Dawuda.
8
Sai ya gina birni kewaye da shi, daga madogaran gini zuwa katangar da take kewaye, yayinda Yowab ya maido da sauran birnin.
9
Dawuda kuwa ya ƙara ƙarfi, domin Ubangiji Maɗaukaki yana tare da shi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options