Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Zedekiah

5 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Magādan Yehohiyakim su ne, Yekoniya ɗansa, da Zedekiya.

  2. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa game da Ahab ɗan Kolahiya da Zedekiya ɗan Ma’asehiya, waɗanda suke muku annabcin ƙarya da sunana. “Zan ba da su ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai kuwa kashe su a gaban idanunku.

  3. Saboda su, dukan masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suke a Babilon za su yi amfani da wannan la’ana cewa, ‘Ubangiji ka yi da mu kamar Zedekiya da Ahab waɗanda sarkin Babilon ya ƙone da wuta.’

  4. Gama sun aikata munanan abubuwa a Isra’ila; sun yi zina da matan maƙwabtansu kuma da sunana suka yi ƙarya, waɗanda ban faɗa musu su yi ba. Na san wannan kuma ni shaida ne ga haka,” in ji Ubangiji.

  5. sai ya sauka zuwa ɗakin magatakarda a fada, inda dukan fadawa suke zaune, Elishama magatakarda, Delahiya ɗan Shemahiya, Elnatan ɗan Akbor, Gemariya ɗan Shafan, Zedekiya ɗan Hananiya, da dukan sauran fadawa.