Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Victories

7 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.

  2. Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”

  3. “Kada a faɗe shi a Gat, kada a yi shelarsa a titunan Ashkelon, don kada ’yan matan Filistiyawa su yi murna don kada ’yan matan marasa kaciya su yi farin ciki.

  4. Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.

  5. Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.

  6. A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.

  7. Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.