Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Thunder

9 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A safiyar rana ta uku, aka yi tsawa, da walƙiyoyi, sai ga girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da suke cikin sansani suka yi rawar jiki.

  2. Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.

  3. Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.

  4. Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”

  5. Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza.

  6. Ubangiji Maɗaukaki zai zo da tsawa da rawar ƙasa da ƙara mai girma, da hadarin iska da guguwa da harshe na wuta mai ci.

  7. Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);

  8. Ba ku zo ga Dutsen Sinai wanda ana iya taɓawa ba, ko ga wuta mai ci sosai, ko ga duhu baƙi ƙirin, ko

  9. ko busar ƙaho, ko ga irin wata murya mai magana da kalmomin da masu jinta suka yi roƙo kada su ƙara ji,