Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Theocracy: Rejected by Israel

4 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Rejected by Israel

  1. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.

  2. Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.”

  3. Amma yanzu kun ƙi Allahnku wanda ya cece ku daga dukan masifu da wahaloli. Kuka ce, ‘Sam, a naɗa mana sarki.’ Saboda haka yanzu sai ku zo gaban Ubangiji kabila-kabila da iyali-iyali.”

  4. “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.