Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The River Jordan: Slaughter of the Ephraimites

3 ayoyi · 31 fannoni

Ayoyi game da Slaughter of the Ephraimites

  1. Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.”

  2. Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,”

  3. sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’ ” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka.