Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Robbers
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”
ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.
Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon ’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji.
Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum, haka ƙungiyoyin firistoci suke; suna kisa a hanya zuwa Shekem, suna aikata laifofi bankunya.
a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje, ’yan fashi sukan yi fashi a tituna;