Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Robbers: General references

6 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da General references

  1. In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;

  2. mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;

  3. za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;

  4. ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”

  5. ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;

  6. gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.