Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Razor

4 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.

  2. Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu.

  3. A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku.

  4. “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi ka kuma yi amfani da shi kamar rezan mai aski don askin kanka da gemunka. Sa’an nan ka ɗauki ma’auni ka kuma raba gashin.