Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Purity

35 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina.

  2. In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.

  3. Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.

  4. Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne.

  5. In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,

  6. balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

  7. Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba.

  8. Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

  9. Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.

  10. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.