Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Probation: None after death

6 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da None after death

  1. Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

  2. “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.

  3. “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’

  4. “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’

  5. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.

  6. Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”