Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pool

5 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Suka wanke keken yaƙi a tafki, a Samariya (inda karuwai suke wanka), sai karnuka suka lashe jininsa, kamar yadda maganar Ubangiji ta furta.

  2. Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda.

  3. Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus.

  4. Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.

  5. Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”