Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pity

9 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Dole ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su gare ku. Kada ku ji tausayinsu, kada kuma ku bauta wa allolinsu, gama wannan zai zama tarko gare ku.

  2. kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi.

  3. Kada ku ji tausayinsa. Dole ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga Isra’ila, don ku sami zaman lafiya.

  4. Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.

  5. In mutane biyu suna faɗa, sai matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don tă kuɓutar da mijinta daga abokin faɗarsa, ta kuma miƙa hannu ta kama marainan wancan,

  6. sai ku yanke hannunta. Kada ku ji tausayinta.

  7. Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā

  8. Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.

  9. Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.