Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mark: Fellow-worker with Paul at Rome
Ayoyi game da Fellow-worker with Paul at Rome
Aristarkus yana a kurkuku tare da ni. Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas. (Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.)
Yesu, wannan da muke kira Yustus, shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni.