Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gilboa

16 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa, sai Isra’ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka kuma karkashe da yawa a dutsen Gilbowa.

  2. Filistiyawa suka abka wa Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kashe ’ya’yan Shawulu. Yonatan da Abinadab da Malki-Shuwa.

  3. Yaƙin ya yi zafi ƙwarai kewaye da Shawulu, har maharba suka ji masa ciwo sosai bayan sun sha ƙarfinsa.

  4. Sai Shawulu ya ce wa mai ɗauka masa makami, “Ka zare takobinka ka soke ni, kada waɗannan marasa kaciya su zo su ci mini mutunci, su kashe ni.” Amma mai ɗaukan makaman bai yarda ba don ya ji tsoro sosai. Sai Shawulu ya zāre takobinsa ya soki kansa.

  5. Da mai ɗaukar makamai ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya zāre takobinsa ya soki kansa ya mutu.

  6. Shawulu da yaransa uku da mai ɗaukar makamansa da dukan mutanensa suka mutu a rana ɗaya.

  7. Sa’ad da Isra’ilawa na bakin kwari da waɗanda suke hayin Urdun suka ga sojojin Isra’ila suna gudu, Shawulu da yaransa uku kuma duk sun mutu, sai suka bar mallakansu suka sheƙa da gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka mamaye wuraren.

  8. Kashegari, da Filistiyawa suka zo domin su washe kayan matattun, sai suka tarar Shawulu da ’ya’yansa uku duk sun mutu, a dutsen Gilbowa.

  9. To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa.

  10. Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa.

  11. Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni.

  12. Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa.

  13. Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu.

  14. Ta haka Shawulu da ’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare.

  15. Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.

  16. Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa.