Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Frugality: General references

10 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

  1. Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.

  2. Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.

  3. Saboda haka sai ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar gari, sai ga wata gwauruwa tana tattara ’yan itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa a tulu don in sha.”

  4. Da ta kama hanya za tă tafi tă kawo, sai ya sāke kiranta ya ce, “Ina roƙonki, ki kuma kawo mini ɗan abinci.”

  5. Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.”

  6. Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Ki tafi gida, ki yi yadda kika ce. Amma da farko ki yi mini ’yar wainar burodi daga abin da kike da shi ki kawo mini, sa’an nan ki yi wani abu wa kanki da kuma ɗanki.

  7. Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,

  8. gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

  9. Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka?

  10. Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”