Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Flattery: General references

9 ayoyi · 20 fannoni

Ayoyi game da General references

  1. Ba zan nuna wa wani sonkai ba, ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;

  2. gama da a ce na iya daɗin baki, da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.

  3. Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka saboda abokan gābana, ka fayyace hanyarka a gabana.

  4. Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya.

  5. Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.

  6. Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,

  7. A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.

  8. Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.

  9. Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu. A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku,