Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Figurative Sieve
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu yana tashi har zuwa wuya. Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka; yakan sa a muƙamuƙan mutane linzamin da zai jagorance su su kauce.
“Gama zan ba da umarni, zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila a cikin dukan ƙasashe kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba.
“Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe kakamar alkama.