Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da False Confidence

5 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.

  2. Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.

  3. Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.

  4. Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.

  5. Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba; dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba. Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa, shi da yake taimako zai yi tuntuɓe shi da aka taimaka zai fāɗi; dukansu biyu za su hallaka tare.