Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ecclesiasticism: Arrogance of

6 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Arrogance of

  1. Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”

  2. Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?

  3. Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.

  4. Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba?

  5. Ina faɗa muku cewa waniwanda ya fi haikali yana a nan.

  6. Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’da ba ku zargi marar laifi ba.