Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Early Rising: Full of minerals

10 ayoyi · 65 fannoni

Ayoyi game da Full of minerals

  1. Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya.

  2. Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.

  3. Mutum ya kawo ƙarshen duhu; yakan bincike zuzzurfar iyaka, yana neman duwatsu a wuri mafi duhu.

  4. Nesa da inda mutane suke zama, yakan huda rami yă yi abin lilo, a wurin da mutane ba sa bi.

  5. Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;

  6. Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.

  7. Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.

  8. Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.

  9. Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.

  10. Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.