Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Compromise: Before litigation, enjoined

7 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da Before litigation, enjoined

  1. kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya?

  2. In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani,

  3. in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba.

  4. “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.

  5. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.

  6. Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku.

  7. Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”