Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cloud of Glory

10 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. sai ɗaukakar Ubangiji ta sauka a kan Dutsen Sinai, kwana shida girgije ya rufe dutsen, a rana ta bakwai, sai Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen.

  2. Ga Isra’ilawa dai, ɗaukakar Ubangiji ta yi kamar wuta mai ci a kan dutse.

  3. Sa’an nan Musa ya shiga girgijen ya hau kan dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba’in da dare arba’in.

  4. Duk sa’ad da aka ɗaga girgijen daga Tentin, sai Isra’ilawa su kama hanya; duk inda girgijen ya tsaya, a nan Isra’ilawa za su yi sansani.

  5. Da umarnin Ubangiji, Isra’ilawa suke tashi. Da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana tsaye a bisa tabanakul, sukan yi ta zamansu a sansanoni.

  6. Sa’ad da girgijen ya ci gaba da kasancewa a bisan tabanakul na dogon lokaci, Isra’ilawa sukan bi umarnin Ubangiji, ba kuwa za su tashi ba.

  7. Wani lokaci girgijen yakan yi ’yan kwanaki ne kawai a bisa tabanakul; da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani da umarninsa kuma su tashi.

  8. Wani lokaci girgijen yakan zauna daga yamma har safiya ne kawai, sa’ad da kuma aka ɗaga shi da safe, sai su kama hanya. Ko da rana, ko da dare, duk sa’ad da aka ɗaga girgijen, sai su ma su tashi.

  9. Ko girgijen ya yi kwana biyu a bisa tabanakul, ko wata guda, ko shekara, Isra’ilawa za su zauna a sansani ba kuwa za su tashi ba; amma sa’ad da aka ɗaga shi, sai su kuma su tashi.

  10. Da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani, da umarninsa kuma sukan tashi. Sukan bi umarnin Ubangiji, bisa ga umarninsa ta wurin Musa.