Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Calf of Gold

19 ayoyi · 20 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma?

  2. Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka.

  3. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ”

  4. Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.

  5. Saboda haka sai ya tsaya a ƙofar sansani ya ce, “Duk wanda yake na Ubangiji yă zo wurina.” Sai dukan Lawiyawa suka taru wurinsa.

  6. Sa’an nan ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Kowane mutum yă rataya takobinsa, yă kai yă kawo daga wannan gefe zuwa wancan cikin sansani, kowa yă kashe ɗan’uwansa, da abokinsa, da kuma maƙwabcinsa.’ ”

  7. Lawiyawa suka yi yadda Musa ya umarta, a ranar, mutane wajen dubu uku suka mutu.

  8. Sa’an nan Musa ya ce, “An keɓe ku ga Ubangiji a yau, gama kun yi gāba da ’ya’yanku da ’yan’uwanku, ya kuma albarkace ku a wannan rana.”

  9. Kashegari Musa ya ce wa mutane, “Kun yi zunubi mai girma. Amma yanzu zan hau wurin Ubangiji; wataƙila zan iya yin kafara domin zunubinku.”

  10. Don haka Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Kaito, mutanen nan sun yi zunubi mai girma! Sun yi wa kansu allolin zinariya.

  11. Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta.”

  12. Ubangiji ya amsa wa Musa, “Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina.

  13. Yanzu tafi, ka jagoranci mutanen zuwa inda na yi zance, mala’ikana kuma zai sha gabanku. Duk da haka sa’ad da lokaci ya yi da zan yi horo, zan hore su domin zunubinsu.”

  14. Sai nan da nan kuma na fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji, yini arba’in da dare arba’in; ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda dā na yi, duka saboda zunubin da kuka aikata a gaban Ubangiji. Ta haka kuka tsokane shi don yă yi fushi.

  15. Na ji tsoron fushi da hasalar Ubangiji, gama ya yi fushin da ku da ya isa yă hallaka ku. Amma na yi roƙo a lokacin, Ubangiji kuwa ya saurare ni.

  16. Ubangiji ya yi fushi sosai da Haruna, har ya yi niyya yă hallaka shi, amma a wannan lokaci, na yi addu’a saboda Haruna shi ma.

  17. Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada.

  18. To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.

  19. Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”