Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Bridegroom

34 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

  2. “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.

  3. “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’

  4. “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’

  5. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.

  6. Yesu ya amsa ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, sa’ad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su.

  7. Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.

  8. Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?

  9. Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”