Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Bread: Multitudes miraculously fed by Christ with

7 ayoyi · 53 fannoni

Ayoyi game da Multitudes miraculously fed by Christ with

  1. Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.

  2. Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.

  3. Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.

  4. Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.”

  5. Ya sa taron su zazzauna a ƙasa.

  6. Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane.

  7. Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.